14 Satumba 2025 - 08:58
Source: ABNA24
Kasar Yemen Ta Tsaya Tsayin Daka Wajen Narkar Da Karfin Makiya

Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari ya sanar a cikin wata sanarwa a jiya Asabar cewa, rundunar sojin kasar ta kai hari kan wasu yankunan Jaffa da ke cikin yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar cewa, rundunar sojin kasar ta kai hari kan wasu yankunan Jaffa da ke cikin yankunan Falasdinawa da Israila ta mamaye.

Ya yi nuni da cewa, a wannan farmakin, an kai shi ne da makami mai linzami na Falasdinu-2 mai dauke da kawuna da dama ya iya kai munanan hare-hare kan wasu a yankin Jaffa da aka mamaye.

Sanarwar ta kara da cewa wannan aiki ya yi nasarar cimma manufofinsa tare da tilasta wa miliyoyin yahudawan sahyoniya neman mafaka. A wani bangare na bayanin ya jaddada cewa: Al'ummar kasar Yemen mai girma duk da zaluncin gwamnatin sahyoniyawan ba za su yi watsi da manufofinsu na goyon bayan 'yan uwanmu Palastinu da ake zalunta da yunwa ba.

Ta'addancin makiya ba zai kara komai ba sai karfafa azamarmu, dagewa da tsayin daka don Allah ga wadanda ake zalunta ba”. Da farko a ranar Asabar, kafafen yada labaran Ibraniyawa sun ba da rahoton cewa, an gano makamai masu linzami na Yemen, kuma an kunna tsarin tsaron sararin samaniyar Tel Aviv domin kakkabo su.

Your Comment

You are replying to: .
captcha